Gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ta kara wa’adin dokar hana fita da shigen jihar ga duk wata motar da ba ta abinci ko magani ba, kuma ta dakatar da duk wasu tarukkan bukin zanen  Suna, da bukukuwan da ake yi a lokacin Aure da ba su zama dole ba, da taron karawa juna sani  don kare kamuwa daga cutar Korona. 

Gwamna Tambuwal tare da Sarkin Musulmi da wasu masu ruwa da tsaki sun sake duba dokar bayan da suka karbi rahoto ga hannun Kwamishinan lafiya Dakta Muhammad Ali Innami.

A cewar  Kwamishina bayan kammala taron da aka rufe kofa ba a bari manema labarai suka shiga ba, kuma a wannan karon ba a gayyace malaman addini kamar yadda aka yi a na farko ba, ma’aikatan da aka ba su umarni su yi aiki daga gida su ci gaba, da kira ga mutanen gari su bar haduwa a yawan taron jama’a.

Ya ce gwamnan ya godewa jami’an tsaro ga irin goyon bayan da suke bayarwa ga hana sabawa dokar hana shige da fice.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *