Spread the love

Gwamnan jihar Bauchi Bala A. Muhammad an auna shi a ranar Alhamis an gano ya warke daga cutar.

Wannan yana zuwa ne bayan kwana 16 da aka tabbatar yana dauke da kwayar cutar.

Gwamnan ya sanar da gwajin na biyu da aka yi masa wanda ya nuna baya da cutar ya warke garau ya fitar da bayanin ne a turakarsa ta Twitter.

Gwamnan ya godewa Allah da dukkan wadanda suka tsaya bayansa a lokacin da yake a killace.

“Alhamdulillah, na samu sakamako mai kyau. Gwajin da aka yimin na biyu na cutar COVID19 ya nuna babu cutar a yanzu. Na gode maku gaba daya da irin addu’o’in da goyon bayan da kuka bani a lokacin ina killace. Mafi muhimmanci gode wa Allah madaukakin sarki.”

“Har wa yau ina godewa malaman addini na jihar nan da wajenta kan dukufa ga yin addu’a ba dare ba rana, ban manta da mutanen da ke kula da cutar a jihar Bauchi da hukumar NCDC” a cwarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *