Spread the love


Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kai gaisuwar ta’aziyar rasuwar Uban ƙasar Geɗawa Alhaji Buba Ɗan galadima wanda yake ƙane ga tsohon gwamnan Sokoto Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, a lokacin da gwamna ya zo wurin gaisuwar Sanata baya wurin.

Dayawan mutane hankalimsu ya karkato kan rashin haɗuwar jagororin biyu a lokacin ta’aziyar duk an san ba wata rashin jituwa ko husuma dake tsakaninsu, abin da wasu ke kallon ko lamarin ya sauya ne.

Managarciya ta yi magana da wani na kusa da Sanata kan lamarin ya ce gaskiya akasi ne aka samu ba tsakanin manyan ba, sai dai yana ganin kamar Furotukul na gidan gwamnati ne suka samar da giɓin.

Ya ce a lokacin da sanata zai bar wurin gaisuwa(gidan margayi cikin garin Wamakko) ba wanda ya faɗa mashi gwamna zai zo, bayan ya dawo daga gidan Kara(gidansa) aka faɗa masa gwamna ya zo, ya ce ba a faɗa masa zuwansa ba.

Ya nuna domin bai san da zuwansa ba ne ya bar wurin, an samu giɓi ne a tsakanin ma’aikata amma ba wani abu a cikin lamarin.

Managarciya ta so ta ji ta ɓangaren Furotukul na gidan gwamnati domin sanin shin ko sun sanar da Sanata kan zuwan gwamna amma bai tsaya ba, ko suna sane da uzurin shi, amma abin ya ci tura.

Lamarin nada ɗaure kai ganin yanda harkokin gwamna suke da tsari da kiyayewa har a ce zai je wuri amma jagoran in da zai tafi bai san da zuwansa ba.


Mataimaki na musamman ga Sanata Wamakko kan harkokin yaɗa labarai Bashir Rabe Mani a bayain da ya rabawa manema labarai ya ce Jim kadan bayan da aka kammala addu’o’in kwana uku, da aka yi yau Laraba, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya godewa dukkan wadanda suka halarta kana ya roki Allah subhanahu wata’ala da ya saka ma kowa da mafificin Alheri.


Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto, ya Kuma godewa shugaba Muhammadu Buhari, da Tsohon Shugaban mulkin sojan kasar nan Janaral Ibrahim Badamasi Babangida, Shugaban Majalisar dattawa ta Kasa Sanata Ahmad Lawan, da sanatoci da dama, tsoffin Gwamnoni da masu ci yanzu kana da ministoci masu ci da Kuma tsoffi, tsoffin sojojin kasar nan masu aiki da wadanda suka yi murabus Hadi da Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa Sanata Bola Ahmed Tinubu.
Sauran su ne, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal  da Mai martaba Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar, da dai sauran Jama’a, wadanda suka yi Masa gaisuwa ta wannan Babban rashin  Dan uwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *