Spread the love

Da yammacin Yau ne Wata kotun majistare dake zamanta a gyadi-gyadi a Kano ta yankewa wasu mutane da ake zarginsu da aikata laifuka daban daban.

Kotun dai ta yankewa mutanen da ta same su da laifi hukuncin zaman gidan Yari amma bayan yanke hukuncin angarzaya da su domin tsare su.

Da isar jami’in gidan yari sai mahukuntan gidan suka ce ba za su karɓa ba.

Mujallar Managarciya ta tuntubi kakakin hukumar Musbahu Lawal kofar Nassarawa in da ya ce tabbas ba za su karbi kowa ba sakamakon karbar Umarni daga Sama.

Tabbas ba za su karbi kowa ba sakamakon karbar Umarni daga Sama.

Abin jira a gani za a saki mutanen ne ko yaya za a yi da su dai managarciya na bin diddigin lamarin don ganin yanda za ta kaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *