Spread the love

 

A cikin shekarar da ta gabata ne dai jarumin ya fitar da sanarwar ficewarsa a masana’antar shirya Finafinan Hausa wadda aka fi sani Kannywood a cikin wani faifan bidiyo da ya fitar.

Ya yanke shawarar ne bayan  hukumar ta tilasta duk wani mai ruwa da tsaki a harkar fim sai yi rijista da su.

A cewar hukumar  rijistar wani tsari ne da zai ba su damar dakile kwararowar baragurbi a masana’antar Kannywood.

Jarumai a masana’antar  da dama  cikinsu har da Adam A. Zango sun bijirewa umarnin na hukumar tace Finafinai, inda suka bayyana cewa babu wanda ya isa ya sanya, su yin rijista da hukumar domin hakan ba ya cikin kundin doka wanda aka kafa hukumar da shi.

Wasu kuwa na ganin an kirkiro tsarin ne da muzgunawa wadanda su ka yi adawa da gwamnatin jihar Kano.

Daga lokacin ne hukumar ta sanya kafar wando da duk wani jarumi ko mawaki da ya bijirewa tsarin na su.

Ko a shekarar da ta gabata hukumar ta haramtawa Zango yin wasan Sallah a garin Kano, kasancewar bai yi rijista da su ba.

Har ila yau idan ba ku manta ba, a cikin watan Fabrairu da ya gabata hukumar ta sake haramtawa Zango shigowa kallon fim din Mati A Zazzau, in da ta sha alwashin kama jarumin matukar ya shigo Kano kallon fim din.

Ana cikin wannan tirka-tirkar  ne kwatsam sai aka ga jarumin  a Talatar da ta gabata, ya wallafa takardar da ke nuni da cewa shi ma ya bi umarnin hukumar na yin rijista da su, abin da ke nufin ya dawo cikin Kannywood da ya fita a baya.

Sauran jaruman da ba su yi rijista da hukumar ba, sun hada da: Sani Musa Danja, Yakubu Muhammad, Mustapha Naburaska, Baban Chinedu, Aminu Alan Waka, Aminu Saira, Falalu A. Dorayi, Naziru M. Ahmad, Abdul Amart Mai Kwashewa, Sadik N. Mafia, da sauran su.

Dalilin Zango na komawa cikin Kannywood wanda ke nuni da yay i amai ya lashe ya nuna ya gano hanyar da ya biyo ba mai bullewa ce ba, jayayya  da hukumar ba abu ne mai kyau ko abin yi ba, yay i haka ne don samun maslaharsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *