Spread the love

Rundunar Yansanda Jihar Zamfara ta gano gidan matsafa tare da rusha shi nan take a Gusau

Daga Aminu Abdullahi Gusau

Kwamishinan ‘yan Sanda jihar zamfara, CP Usman Nagogo a yau ya baje kolin wasu kayan Tsafi da jami’an sa suka gano a wani gida da ake zargin ana tsafi a ciki bayan samun rahoto daga mutanen anguwar.

Nagogo ya baje waɗannan kayan ne, ga manema labarai, a hedikwatar ‘yan sanda dake unguwar Gwaza, inda yace an samu dukkan kayan na tsafi a unguwar Dallatu ne, bayan sabuwar tashar Mota a Gusau babban biirnin Jihar, inda nan take aka rushe gidan bayan fitowa da kayan tsafi dake ciki.

Kwamishinan yan sandan yace lokacin da jami’an ‘yansanda suka isa gidan da dare, hasken motar su yasa wasu mutane biyu dake aikin tsafin sun ranta cikin na kare ba a samu kama su ba.

Cikin abubuwan da aka kama a wannan gidan sun hada da, wata kwarya wadda ke cike da jini, da kuma mangal Karami cike da gawai da turare an zuba a sama ga wata leda cike da kyallaye kaloli daban-daban da wani butum-butumi da wata kwarya mai rubutun Arabi an yanka ta kamar hullar kwano.

Sauran kayan tsafi da aka kara bankadowa akwai wata kwarya kuma cike da wasu ruwa an daura mata wani abu kamar Jigida itama da rubutun Arabi a jikin tukunyar, da dai sauran su.

Ata bakin kwamishinan, Jinin da aka samu cikin kwarya har yanzu ba a san ko jinin mine ne ba, amma yace za su aika da shi Asibiti don gano masu jinin Mutum ne ko na Dabba.

“Kayan fa suna da yawa, saboda akwai wasu takardu, waɗanda ke dauke da sunayen manyan ‘Yan siyasar wannan jihar waɗanda suna cikin wannan gwamnati mai ci yanzu, amma bazan bayyana sunan mai gidan ba, sai mun kare bincike.”inji Nagogo.

Harkar tsafi a jihar zamfara ba bakon abu ba ne, kasan cewar tun kafin hawan wannan gwamnati ta Bello Muhammed Matawalle, an taba jefa Alkur’ani mai girma a cikin najasa ta magewayi, kuma an kama masu laifin, hakama a wannan gwamnati irin wannan masifar ta kara faruwa, inda nan take gwamnati ta rufe wannan makarantar kuma aka kafa kwamitin bincike.

Hakama watannin baya aka kunnawa makabarta wuta duk a garin na Gusau inda ake zargin duk matsafan ne keyin wannan aika aikar domin biyan bukatun su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *