Spread the love

Wata Unguwarzoma ko uwar biki wadda aikinta ne karbar haihuwa ma’ana duk mace lokacin haihuwarta ya zo ta fara nakuda akan kira ta ta zo domin taimakawa mai haihuwar da abin da za a haifa ya rabu da mahaifa lafiya ya zo duniya ba matsala uwar ta samu sauki haife abin cikin taimakon da aka yi mata, a wannan karon an samu akasi ta fizge kan jaririn da za a haifa lokacin da take karɓar haihuwa.  

Wannan Lamarin dai ya faru ne a unguwar Rimin kebe a karamar hukumar Ungoggo  dake jihar Kano in da ake zargin unguwar zomar Wata ma’aikaciyar lafiya  ce da cire kan jariri. Kamar yadda majiyar ta labartawa managarciya. 

Da fari dai angayyato ta ne domin karbar haihuwar da ta bayyana sai ta fara aikinta in da jaririn kansa ya leƙo Ko da ganin haka tasa hannu ta jawo kan sai gashi a hannunta ita kuma gangar jiki tamaƙale a ciki. 

Nan da nan hankali ya tashi daga bisani aka garzaya da mai jego zuwa Asibitin Nassarawa.

A halin yanzu dai wadda ake zargi da wannan ɗanyan aikin ta tsere.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *