Spread the love

Sati daya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiyana rufe Abuja da Lagas da Ogun ba a yawo da yin kowace ma domin tsoron yaduwar cutar COVID 19, da yawan wasu mutane sun dawo da cigaba da harkokinsu na yau da kullum.

Da yawan mutanen dake wajen birnin Abuja sun dawo harkokinsu na yau da kullum, a bude kasuwanni da wasu shagunan da ake sayar da kayan da ba su shafi wadanda aka ware ba na amfanin rayuwa a ungawannin Lugbe, Kuje, Bwari, Nyaya ko Karu da sauransu, da yawan mutane sun ba da dalilin sabawa dokar da suka yi saboda yunwa ne.

Karamar Ministar Abuja Ramatu Tijjani ta bayyana cewa gwamnatinsu za ta fara rabon kayan tallafi ga maras karfi a cikin wannan satin.

Ministar ta ba da sanarwar ne a wurin rangadin da fita a sansanin masu bautar kasa dake Kubwa.

A jihar Lagas ma an samu wasu mutane da suka bijirewa dokar suka tafi yin harkokin gabansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *