Spread the love

Hukumar tace Finafinnai ta jihar Kano karkashin shugabanta Ismail Na Abba Afakalla ya ba da sanarwar dakatar da haska shirin Kwana Chasa’in dakuma shirin Gidan Badamasi.

A binciken da mujallar managarciya ta gudanar ya nuna hukumar ta yi haka ne Saboda wani ɓangare da aka nuna a cikin shirin a makon daya gabata.

Majiyar ta shaidamana cewar mutane da dama sun kalubalanci abin da ya faru.

Dokar hukumar ta sheaka ta 2001 ta yi nuni da cewar kowane shirin da za’a fitar kuma za’a haskawa mutanan Kano dole ne a tantance shi.

Wannan shirin yana ɗimbin makalla da ke bibiyarsa domin tsaruwarsa da dacewarsa da yanayin da ƙasar Nijeriya ke ciki, shirin ya karɓewa finafinnan Hausa na dake kan faifan kallo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *