Spread the love

Gwamnan Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga mutanen jiha musamman wadan da ke cikin kananan hukumomi da su kawo rahoton duk wani dan kwangila da aka baiwa aiki a kauyukkansu da ya gudu ko yake yi wa aikin tafiyar  hawainiya don daukar matakin da ya dace.

‘Duk aiyukkan da ake yi muna yin su ne don amfanin jama’a kai tsaye don ba wata hujja da mutane za su rika yin biris da abubuwan da aka samar masu yakamata su sani fa na su ne da yakamata su kare daga barnatawa da lalatawa duk wani aiki da ya samu inganci da kulawa bai kamata su bari ya shiga mawuyacin hali ba’ a cewar Tambuwal

  Wannan bayanin ya yi shi ne tun farkon wa’adin mulkinsa na farko kan kujerar gwamnan jihar Sokoto.

Bayanin ya fito ne a tabakin mai Magana da ya wun  gwamnan Margayi Malam Imam Imam(Allah ya jikansa da rahama) ya ce gwamnan ya yi kalaman  ne a lokacin da ya yi taro da shugabannin kananan hukumomi 23 na jiha.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *