Spread the love

Domin kariya ga wanzuwar cutar Korona Sanata Aliyu Magtakarda Wamakko ya fara rabon man wanken hannu guda dubu 12 ga magidanta a faɗin ƙananan hukumomi 23 na jihar Sokoto.

Wannan yunƙurin ya yi shi ne don goyon bayansa ga ƙoƙarin daƙile cutar da gwamnatin Nijeriya ke yi da ta yi sanadin salwantar rayuwar a duniya.

A Nijeriya akwai kes ɗin cutar 224 ga mutane a faɗin ƙasar gaba ɗaya.

Tallafin mataimaki na musamman ga Sanata Wamakko kan harkokin matasa da ɗalibai Suleiman Mahmud Tijjani, a bayanin da mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai Bashir Rabe Mani ya fitar ga manema labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *