Buhari Ya Bada Umarnin Rabawa Talakawan Nijeriya Tirela 150 Na Shinkafa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya ba da umarnin raba manyan motoci guda 150 na shinkafa da kwastam din Najeriya suka kwace a kwanakin baya, ga jihohi 36 na kasar nan kamar yadda VANGUARD ta ruwaito.

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ce ta sanar da hakan yayin da ta ke karbar tambayoyi daga manema labarai a wani taro a Abuja, ta ce, an mika motocin shinkafar da aka kama ga ma’aikatar kula da ayyukan jin kai da misiba domin rabawa ga ‘yan Najeriya.

Abin jira a gani sanda za a fara rabon da yadda rabon zai kasance domin kowa ya samu ko mafiyawan talakawan su samu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *