Spread the love

Bayan kammala harkokin shari’a kan zaɓen 2019 gwamnan Zamfara Bello Matawalle yana cikin matsin lamba sai ya bar PDP ya koma APC.

Tsohon gwamnan Zamfara Ahmad Sani Yarima shi ne wanda ya faɗawa mutane ana yin matsin lambar ga gwamnan ya shiga APC.

Matawalle shi ne babban wanda ya ci gajiyar matsalar jam’iyar APC wanda rikicin cikin gida ya sanya ta rasa kujerunsu, ana son gwamnan ya canja sheka.

Yarima ke jagorancin wannan yunƙurin na shigo da Matawalle APC, jam’iyar ta so ta karɓi jihar a kotun ƙoli amma lamarin ya ci tura.

A wata firar da aka yi da Yarima ya ce nan ba da dadewa ba Matawalle zai shigo jam’iyar ta APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *