Spread the love

Mariya Tambuwal  haifaffiyar  garin Sanyina ce, wadda aka haifa a ranar 27 ga Afirilun 1978, cikin karamar hukumar mulkin Tambuwal, ta yi karatun Firamare dinta a Firamaren Sanyinna,  bayan ta  kammala ne ta wuce makarantar mata ta Illela (Unity Girls Secondary School Illela) tana gama sikandare, ba ta tsaya ba ta wuce kwalejin kimiyya waton Umaru Ali Shinkafi polytechnic ta yi difiloma kan fannin shari’a a 1993-1995(diploma in law). 

A  lokacin da mai gidanta ya samu zama kakakin majalisar wakillai ta kasa (2011-2015) ta kara daure damara da sadaukarwata a gare shi domin cimma burinsa na rayuwa, a  kokarin  mace ga mijinta don samar da iyali da al’umma tagari. Ta kirkiro shiraruwan  cigaban mata da matasa da tallafin ilmi da wayarwa  mata  kai kan sha’anin kiyon lafiya musamman mata masu renon ciki da  kananan yara.

Allah mai iko a lokacin da jagorancin mutanen jihar Sakkwato ya hau kansu, uwar gidan gwamna ta rungumi aiki babu kama hannun yaro ta fito da abubuwan cigaban yara da ba su nishadi, takan je makarantu ta gani da idonta halin da ake ciki. Bata tsaya anan ba ta kutsa kanta ga samar da hanyoyin wayar da kai,  domin samun zaman lafiya tsakanin kabilu daban-daban, da wannan tunanin nata ne, ta sanya hikima cikinsa in da ta ke shirya buda bakin azumin Ramadan, da shirya muhawarorin ilmin dalibai ‘yan makaranta, ga kuma tsaya wa  a ji koken jama’a a ta hanyar tattaunawa da jagororinsu da su kansu talakawa a cikin sakin fuska da annashuwa, kusan ba ta da wani lokaci na hutawa ko shakatawa ko yawon buda ido wanda ya wuce ziyarar marar sa lafiya, gajiyayyu da kuma marar sa galihu,mafi yawancin lokutta a duk sadda take cikin nishadi takan ziyarci Marayun Allah ta ci abinci tare da su domin ta faranta musu rai susan cewa suna da gata a cikin al’umma, wannan dalilin ne ya sanya ake kiran ta da suna Uwar Marayu.

Uwar Marayu dai burinta Matasa, Mata da kuma Marayu a jihar Sakkwato su samu walwala da farinciki a zamanin mulkinsu, halayyar da ta bambanta ta da dukkan matan gwamnonin Nijeriya.

Hajiya Mariya ta kirkiri wata GIDAUNIYAr sa kai,  don kara inganta taimakon mata da kananan yara da marasa galihu a cikin alumma da hukuma ta aminta da ita mai suna MARIYA TAMBUWAL DEVELOPMENT INITIATIVE (MTDI) ta yi haka ne don taimakon ya tsayu da kafafunsa ya iya shiga a kowane lungu da sakon Sakkwato,

Kalubalenta na rayuwa

Kalubalenta bai fi rashin fahimtar da ke ga mutane na bambancin gidauniya da gwamnati ba duk abin da gidauniya tayi sai a dauka na gwamnati ne; basu fahimci cewar gidauniya tana marawa ayyukan gwamnati ne ba, domin kawo cigaba mai amfani, amma alhamdulillahi an fara fahimta allah ya kara yi muna jagora.

Darasin da ta koya na rayuwa.

“To kasan rayuwa mai juyawa ce koyaushe, ko ta zo da abu mai kyau ko akasinsa, amma dai kowane mutum yana   bukatar ya samu rayuwa mai kyau a kullum, hakan ne zai jagorance shi a samun nasara, darasin rayuwa ya kara sanya ni, rike gaskiyar da na taso da ita a cikin kowane lamari, don na tabbatar duk wanda ya rike gaskiya ba zai fada halin danasani ko kaico ba.”

“Burin da nake da shi bai wuce na zama mai nutsuwa da hankali, da yiwa yarana tarbiya kamar yadda aka yimin; kuma ina da kudurin ganin mata ‘yan uwana sun tsayu da kansu yara kanana sun daina barace barace. ilimin yara mata ya inganta a karkashin gidauniyata da yardar Allah. ” a cewar Mariya Tambuwal.  

Da ta juya kan rawar da mata kan iya takawa a cikin al’umma ta ce  ‘A lafiyayyen hankali mata da maza ba daya ba ne, amma mata suna da rawar da za su iya takawa ga al’umma, don su ne kashin baya al’umma, masu iya magana sun ce karantar da mace karantar da al’umma ne.’ in ji uwar gidan gwamna.

Taimakonta ga marasa galihu a jihar Sakkwato

Taimakawa mata masu cutar yoyon fitsari a asibitin Maryam Abacha, lokaci-lokaci domin ganin masu cutar sun samu gudunmuwar da ta dace su san su ma mutane ne kamar kowa, da kuma shirya tarurruka daga lokaci zuwa lokaci dmin wayar da kan matasa akan rashin amfanin shaye shaye wanda hakan yayi  sanadiyar bude center ta warkar da masu shaye shaye a asibitin specialist wanda ta yi tare da hadin kan matan gwamnonin Arewa; tana kuma ba da tallafi ga yara mata a kai kai da kungiyoyin addinin musulunci domin su ci gaba da fadakarwa; tana kuma aiyukka da kungiyoyin turawa domin taimkawa ta haujin lafiya kamar su  UNFA,plan ;USAID  da sauransu.  

Daga karshe tana kiraga matasa da su daina dabi’ar area boys su je makarnta suyi karatu domin a dama da su kuma a yi alfahari da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *