Spread the love

Daga Sadiya Attahiru.

Matakin da Farfesa Yemi Osinbajo ya dauka na sallamar tsohon Darakta Janar na hukumar tsaro na farin kaya(DSS) Lawal Daura daga aiki, a lokacin da yake mukaddashin shugaban kasa, kan kawanya da jami’an DSS suka yi wa majalisar dokoki ta kasa, abin yabawa ne ganin abin da aka aikata yana tarnaki ga cigaban dimukuradiyar Nijeriya, ba a taba ganin haka ba,tun bayan da kasar ta dawo saman wannan turba a 1999.

Majalisa ita ce ginshiki na dimukuradiya da ita ne ake gane cigaban duk wata kasa mai kurarin tana aiwatar da dimukuradiya; yadda yakamata, a tun ranar da aka yi wannan wasan kwaikwayon, an yi ta yada labarai kan lamarin da yadda kowa ke kallonsa, kan haka Managarciya ta yi nata hasashen a yanzu bayan dogon lokaci da aka dauka da sallamar da aka yi wa Dauran.

Wasu na kallon Daura a lokacin yana saman kujerarsa ya hada kai da tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki suka kunyata gwamnatin tarayya kan yunkurinta na tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin  cikakken shugaban hukumar yaki  da cin hanci da rashawa da sama da fadi da dukiyar jama’a(EFCC) yayin da wasu ke ganin aikinsa ne ya yi amtsayinsa na ma’aikacin gwamnati da ya yi alkawalin rike amanar gwamnati ba sanya son rai.

Tura jami’an da yayi sanadiyar raba shi da aikinsa, akwai rahotanni da aka samu cewa shi Dauran da shugaban jam’iyar APC sun yi zama da  sanatocin APC a ranar Litinin kan shirinsu na tsige shugabannin majalisa, in rahotannin gaskiya ne, rumfa shi ta farma kenan? Don tseratar da martabar kasa.

Muna iya tunawa 7 ga watan Oktoba na 2016 yanda jami’ansa suka yi dirar mikiya a gidajen manyan alklan kasa, aka kama bakwai daga cikinsu da zargin almundahana, abin ya haifar da rashin jin dadi a bangaren shari’ar har suka yi alawadai da lamarin cewa ya sabawa  tsarin shari’a da dimukuradiya.

Tun lokacin da aka sallame shi daga aiki ba a sake jin duriyarsa a harkokin gwamnati ba, abin da ya baiwa mutane mamaki ganin yanda yake cikin na hannun damar shugaban kasa Muhammadu Buhari, an sa ran a cigaba da ganinsa a cikin harkokin mulki musamman a fadar shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *