Spread the love

Al’ummar Abena na karamr hukumar Doma a jihar Nasarwa sun shiga cikin damuwa yanda aka tashi da labarin matar aure Rosemary Osegba ta shake  surukarta Mista Ashi Chem, abin da ya kaita ga rasa ranta kan zargin tana yi mata katsalandan a cikin harkar aurensu.

Katsalandan take yi mata ga mijinta Abaagu Chem shi ne ya sanya aurensu ya samu matsala yam utu.

Matar tana ganin ba ta da wata hanya da za ta iya tseratar da aurenta in ba ta kashe uwar mijinta ba.

Rosemary ta auri mijinta mai sana’ar noma da tireda tun shekarar 2016 amma ba su samu haihuwa ba, mijinta mai shekaru 43 shi kadai ne ga mahaifansu ya rasa mahaifinsa tun yana dan shekara 18.

Abin da ya sa ake ganin mahaifiyarsa taki son su cigaba da zaman aure duk da mijin yana son matarsa.

Ba ta da wani dalili na kasha surukarta sai don a ta cigaba da zama da mijinta tun da ita ba ta son zaman, don haka ba ta dana sanin abin da ta aikata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *