Spread the love

Dakta Zainab Atiku Bagudu ta aika da tawaga wajen ganin lafiyar wadansu yara tagwaye da wata uwa da ba ta da tausayi ta jefar a unguwar Gesse 3 dake cikin Birnin Kebbi a jihar Kebbi.

Ta aika da tawagar masu jinkai karkashin jagorancin Mai baiwa Gwamnan Kebbi Shawara kan harkokin mata da yara Hajiya Zara’u Wali tare da P.A din Dakta Zainab Bagudu Hajiya Balkisu mai Ahu sun gana da mai unguwar da aka kai jariran gidan sa wanda ya yi alƙawali zai rike yaran amana a gidansa ba sai an kai su gidan marayu ba.


An yiwa yaran Immunization dama sauran duk wata kulawa ta lafiyar yara sabuwar haihuwa da suke bukata.

Haka kuma tawagar ta karantawa Mai unguwar sharuddan kula da iyali musaman marayu inda mai unguwa ya amince da sharuddan da aka zayyyana masa abin da yasa aka barwa Mai unguwar kulawa da yaran.

Daga nan Mai baiwa Gwamnan Kebbi shawara Hajiya Zara’u Wali ta nuna jin dadinta da jin abin da mai unguwa ya fada
Saboda sakin jiki da mai unguwa yayi da son rike wadannan yaran zai sa wadda ta yi wannan mugun aiki za ta koma da ta sani aikata hakan nan gaba.

Daga nan Maibaiwa Gwamna Shawara Hajiya Zarau Wali tace insha Allahu matar Gwamnan Kebbi Zainab Atiku Bagudu za ta dinga zagayowa domin sanin halin da jariran nan suke cikin saboda a kodayaushe bukatun matar gwamnan shi ne ta ga kowane iyalai sun samu kulawar da ta dace da bukatunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *