Spread the love

Shugaban Majalisar malamai na ƙasa na ƙungiyar Izala Sheikh Sani Yahaya Jingir ya karyata maganganun da wasu jama’a ciki har da malamai na cewa ya bijirewa dokokin gwamnati a jihar Filato, wanda ba haka nan ne ba gwamnatin Filato ba ta hana su je sallar jumu’a ba kuma sai da sanin gwamnati ne suka fita sallah.

Sheikh Jingir ya ce duk wata doka da ka’ida da aka sa a jihar Filato sai da ya bi ta kafin gudanar da sallar Juma’ar.

Sheikh Jingir ya ci gabada cewa makiya musulunci da munafukai ne ke sukarsa akan ya yi sallah kuma ya ce ransa a hannun Allah yake kuma addininsa ya fi rayuwarsa, ba zai bar sallah saboda wani hasashe na siyasar duniya.

Ya ce akan sallah an tare shi da jama’arsa a rukuba za a hallaka shi amma Allah ya tsare shi. Haka aka kawo masa hari yana tafsir a massalacin ‘Yan Taya Jos, hakan ba zai sa shi razana ba.

Sheikh Jingir ya ci gaba da cewa kafirai da munafukai za su taru a kan sai sun hana Sallah kuma Allah ba zai ba su nasara ba.

“Mu muka ce a zabi Buhari da Lalong ba don sun ba ni kudi ba sai don cancantar su kuma duk wata doka da za su kawo don tsare rayukan da dukiyoyin al’umma ina basu hadin kai”, cewar Sheik Jingir.

“Duk wanda ya ce ba ma bin dokar gwamnati Allah ya isa tsakaninmu da shi”, a cewar Sheikh Jingir a yayin da yake gabatar da nasihar Juma’a a masalacin ‘yan taya dake birnin Jos.|

A satin da ya gabata da Malamin ya jagorancin sallar jumi’a tare da mabiyansa aka yi ta maganar ya saɓa wa umarnin gwamnati domin wasu masallatai a birnin ba su yi sallar jumu’ar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *