Spread the love

Ba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II ne ya raba buhunhuna masu hotunansa ba.

Hajiya Sa’adatu Baba Ahmad ce ta wallafa wannan bayani a turakarta facebook domin sanar da jama’a halin da ake ciki kan rabon shinkafa da motocin da ake gani masu hotunan Mai martaba Sarkin Kano Mhammad Sanusi ll na neman ya shiga siyasa har ma ya yi takarar shugaban ƙasar Nijeriya.

A bayanin ta ce tabbas Sarki Sanusi II ya sa an raba kayan abinci ga mabukata amma ba mai hotunansa a jikin buhunhuna ba, wadannan hotunan buhunhuna masu hoto da motoci masu hoto hakika bamu san wanda yake yinsu ba, ko da masoyan sarki ne ko da makiyan sarki Sanusi ne to, sun yi ne don kansu domin shi dai sarki har zuwa yau ba shi da niyyar shiga ko wacce jam’iyya ko tsayawa takarar siyasa.

Sarki yana godiya ga masoyansa tare da yi musu fatan alheri. Allah ya taimaki sarki Allah ya bar sarki da masoyansa
Wannan shi ne ƙarshen bayanin da Sa’adatu Baba Ahmad ta wallafa.

Wannan rubutun nata ƙarara ya fito da bayanin wasu ne ke yin wannan hobɓasa domin su janyo hankalin sarki ga shiga harkar siyasa kan manufar da suke da ita ga Nijeriya.

Abin jira a gani za su iya shawo kansa ya shiga siyasa ko akasin haka lokaci ne zai bayyana haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *