‘Yan sanda a jihar Sokoto  sun samu nasarar kama wani matashi da ya mayar da kanshi mace yana yaudarar maza ya karɓi kudinsu da sunan za su tafi su yi amfani da shi, sai ya yi dubarar da zai sulale ba tare da bukatar wadan da suka bayar da kudin ta cika ba.

Matashin Mai suna Muhammad Aliyu dan shekara 23 mazauni unguwar Marina a karamar hukumar Sakkwato ta kudu, an kama shi sanye da kayan mata yana jiran wani da zai zo ya neme shi da sunan shi mace ne a harabar Faƙon idi a birnin jihar.

A bayanin da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ASP Muhammad Abubakar Sadik ya fitar ga manema labarai ya ce wanda aka kaman ya ce yana yaudarar maza ne domin ya samu kudi a hannunsa. Ya ce da zaran sun kammala bincike za su kai shi kotu.

Wakilinmu ya zanta da matashin bayan da hukumar ‘yan sanda ta fito da shi in da aka tsare shi ya ce ‘yan sanda sun kama shi sanye da tufafin mata yana tsaye kawai bayan sallar Magriba  amma shi ba kowa yake jira ba kuma shi dan daudu ba ne.

“Na sanya tufafin mata ne domin in samu kudi don na fahimci mata ne suka fi samun kudi a wurin maza, na yanke shawarar gwada hanyar domin ina da burin mallakar wayar hannu ta kece raini dana samu kudin sayen wayar ko ‘yan sanda ba su kama ni ba zan bar wannan dabi’ar amma ban yi nasara ba, naira  550 ne kawai na samu hannun wani sauka kamani.” A cewarsa.

Ya aka yi ka samu kudin hannunsa? Ya ce “Ina tsaye ya zo ya ganni ya ce min yana son mu tafi daki sai ya bani kudin in same shi a daki, ni kuma banje ba.”

Wata majiyar ta tabbatar wa Aminiya wannan matashi ya mayar da wannan harkar abin yi tsawon lokaci in ya hadu da wasu fasikan maza sai ya yaudare su da sunan shi mace ne da ya karbi wani abu a hannunsu ba su kara ganinsa, har sana’ar kalwancin mata yana yi wa wasu kafin a kama shi, tuburan jahili ya tashi ba karatun boko da Arabiya  kamar wanda ya san shi ya tabbatar.  

Jami’an ‘yan sandan Dadin kowa ne suka kama matashin a lokacin da suke sintiri na duba halin da garin yake ciki da kuma mafakar ɓata gari.

Majiya: jaridar Aminiya. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *