Spread the love

Minista mai lura da jin ƙai da walwalar Jama’a Hajiya Sadiya Umar Farouk ta shaidawa manema labarai cewar ya zuwa yanzu fiye da magidanta miliyan biyu da dubu dari shida ne suka amfana da tallafin dubu ashirin da gwamnatin tarayya ta ba da umarnin a rabawa ‘yan kasa saboda rage radadin zaman gida.

Ministar ta ce rabon zai cigaba a jihohin Nijeriya domin ganin talakan ƙasar nan ya fita daga cikin raɗaɗin da yake da shi.

Da yake ministar haziƙar mace ce nai kishin aikin da take yi wanda hakan ya sanya nauyin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ɗaura mata ba dare ba rana burinta a ce madalla ta ga ta sauke lamarin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Ministar tana son aiyukkan jinƙai da taimakon jama’a abin da ta taso kan shi kenan wanda shi ne ya yi jagorancinta ga samun nasarar aiyukkan tallafin jama’a mabuƙata da take yi tsawon lokaci.

Minista Sadiya tana cikin kwamitin da shugaban kasa ya kafa don kula da ciwon Korona da daƙile shi da ɗaukar mataki na wayar da kai har a tabbatar da an kashe ciwon a Nijeriya.

Ministar ta yi kira ga ‘yan Nijeriya su bi shawarwarin likitoci kan rigakafin kamuwa da cutar ta Korona, ta ce a riƙa waken hannu a kai akai da man senitaza a guji shiga cunkoson mutane da kuma kowa ya zauna gida don kariyar kai da sauran shawarwarin da aka bayar don kare kai da ƙasa ga wanzuwar wannan anoba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *