Spread the love

 

Annobar cutar Korona da aka yi wa lakabi da(covid19) gwamna 19 da ke cikin gwamnoni 36 a Nijeriya ba a san komi game da labarin sun kamu da cutar ko ba su kamu ba, an dai yi shiru ba a bayyana komi ba a kai, abin da ya sanya mutanen jihohin da gwamnonin suke ke neman a yi masu karin haske don sanin makomarsu da ta jihohinsu.

Shugaban kungiyar Gwamnonin Nijeriya Dakta Kayode Fayemi ya shawarci ‘yan uwan nasa da su tafi a auna su don irin muhimmancin da suke da shi.

Gwamnonin da har yanzu ba a bayyana matsayar da suke ciki ba su ne: Gwamnan Akwa Ibom da Revers da Dalta da Enugu da Zamfara da Sokoto da Jigawa da Adamawa da Taraba da Lagos da Gombe da Kwara da Yobe da Benue da Ebonyi da Kogi da Imo da Abia da Filato.

Haka kuma Gwamna uku ne suka kamu da cutar Gwamnan Bauchi Bala Muhammad da Kaduna Nasir El-rufa’i da Oyo Seyi Makinde.

Da yawan mutanen Nijeriya sun yaba ma wadan nan gwamnonin kan abin da suka yi domin zai kara karfafa mutanen kasa su tafi a rika auna su don su tabbatar da halin da suke ciki.

Cibiyar kula cirutoci ta kasa ta rubuta wa gwamnonin su killace kansu tare da shawarwarin da aka ba su.

Jaridar daily trust ta tabayyana an fitar da sakamakon gwajin da aka yi wa Gwamnoni 13 da aka tabbatar ba su dauke da kwayar cutar, su ne Gwamnan Kebbi da Katsina da Osun da Ekiti da Edo da Bayelsa da Ogun da Ondo da Nasarawa da Neja da Cross River da Borno da Anambara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *