Spread the love

Sarkin Musulmi ya yi alkawalin goyon bayan Kungiyar Zawarawa da marayu da aka kaddamar a Sakkwato

Muhammad Nasir

Sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi alkawalin goyon bayansa ga Kungiyar taimakon mata zawarawa da marayu wadda ake Mar’atussaliha, ya ce kungiyar tana dauke da alheri da  ba zai bar irin wanna aikin ya tafi ba tare da ya sanya nasa abin da yake iyawa ba.

Sarkin Musulmi ya yi wannan kiran ne ta bakin wakilinsa Sarkin yakin gagi Alhaji Umar Jabbi a wurin bukinkaddamar da shugabaannin kungiyar na jihhar Sakkwato wanda ya gudana a dakin taro na makarantar hardar Kur’ani ta Sarkin musulmi Maccido a satin da ya gabata.

Sa’ad Abubakar ya yi kira ga mutanen kasar nan su dawo daga rakiyar sayen magani a kasashen waje su rika sayen na gida Nijeriya ganin akwai wadan da ke yin maganin da inganci da kuma sahihan itatuwan magani, hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasa da basirar da ‘yan kasa suke da ita.

“Mutane nada rauni sosai a wurin bayar da gudunmuwar aiyukkan alheri hakan bai dace ba abin da ka bayar a taimaki maraye ko wata mace dake bukatar tallafi domin wani hali da take ciki shi ne naka ba wanda ka kashe a wajen sayen motoci da gidaje ba. Don haka neke kira ga al’ummar kasar nan su himmatu ga aiwatar da aiyukkan tallafawa marayu da mata mabukata, ka da abar irin waddan nan kungiyoyi hakan ba karfafa musu domin al’umma na da bukatarsu” a cewar Sarkin Musulmi.

Da farko Shugabar Kungiyar ta kasa da kasa Malama Khadija Muhammad Salau a jawabinta ga mahalarta taron ta yi bayani kan manufar kungiyar jinkan marayu da Zawarawa, kuma kungiyar ta shafe shekarru 15 da kafuwa, amma shekara daya da ta gabata ne aka yi mata rijista da hukumomin gwamnati da suke da alaka da kungiyoyi irin wadan nan.

Ta ce ta fara kungiyar ne da mutum 50 har suka kai 100 a jihar Kano a yanzu ba tasan adadin yawan mambobin kungiyar ba don a yanzu tana da rassa a jihohin Bauchi da Kebbi da Sakkwato da Kano bayan kasar Togo da Burkinfaso da Nijar da Mali da Ghana da Benin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *