Spread the love

Mahara wadan da ake zargin ɓarayin shanu ne  sun shuga ƙauyen Gangara dake cikin karamar hukumar Sabon Birni a Sokoto sun kashe mutum 22 suka shace shanu sama da 1500, bayan sun kone kasuwar garin gaba ɗaya sun raunata ɗimbin jama’ar garin da makwabtansu.

Maharan maza da mata ne saman babura sun kai 30 kowane mashin yana dauke da mutum uku a samansa sun shigo da La’asar ta jiya Laraba sun tafi da shanu da tumakai masu yawa. ‘Yan Sanda Sokoto sun tabbatar da faruwar harin tare da gano gawar mutum  22 da maharan suka harbe a lokacin da suka shigo garin a harbin mai kan uwa da wabi.


A bayanin da jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Muhammad Sadik Abubakar ya baiwa manema labarai a jihar  ya ce a yunkurin da jmi’an tsaro suka yi na kama maharan sun raunata wasu daga cikin maharan har sun harbi daya daga cikinsu abin da ya yi sanadin mutuwarsa ‘yan  uwansa sun shige daji ba a samu kama su ba.


Mutanen garin suna cikin tashin hankali kan wannan harin da aka kawo masu ba zato ba tsammani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *