Spread the love

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum a yau Alhamis ya kwace lisisin wasu gidajen mai guda 10 kamar yadda Daily Nigeria ta ruwaito saboda sun ɓoye man da ya kamata su sayarwa mutanen jihar.

Gwamnatin Jihar ta kwace lasisin gidajen man fetur din ne sakamakon samun su da laifin boye man don jiran sai ya yi tsada su sayarwa al’umma wanda hakan ya saɓawa dokokin ƙasa rashin tausayi ne kuma.

A wani zagayen ba za ta da gwamnan ya gudanar cikin garin na Borno ya gano hakan da kan sa shi ya sanya ya karɓe ladisinsu na wuccin gadi don su gyara halinsu in ba su yi ba suna iya rasa lasisin gaba ɗaya.

Sakataren gwamnatin jihar, Usman Jidda, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri, ya ce kwace lasisin gidajen man ya yi daidai da ikon da aka baiwa gwamnan a karkashin dokar Kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *