Spread the love

Gwamnan Bauchi ya koyi darasi a zaman kaɗaici da yake yi kan cutar Korona, ys kuma godewa duk waanda ya taya shi alhinin wannan jarabawa da ta same shi, musamman malamai da ke yi masa addu’a.


Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammed Kauran Bauchi ya yi wa al’ummar jihar jawabi ta hoton  bidiyo daga in da ya killace kansa yake Aman kaɗaici bayan ya kamu da cutar Korona in da ya bayyana cewa, ya koyi darasi daga wannan cuta kuma da zarar ya fito, mutanen Bauchi za su ga wani sabon Kaura mai adalci a halin yanzu lafiyarsa ƙalau.


Gwamnan ya yi wannan alwashin a sabon bidiyon da ya wallafa a jiya laraba, in da ya kara jadda cewa; zai zama mai matukar adalci bayan ya fito daga wannan cutar  da ubangiji ya jarrabe shi da ita. Inji shi.


Yanda cutar take ga mutanen Nijeriya da haka ta zama a duniya da ba ta fitini duniya ba, da fatan Allah ya tafiyar da ita gaba ɗaya ya kawo sauki da gushewarta a duk in da ta wanzu ya kare in da babu ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *