Spread the love

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya gargaɗi malaman addinin musulunci a Nijeriya kan durmuyar da mabiyansu da suke yi ba su bari su fahimci gaskiya game da annobar Gubar Korona.

Sarkin musulmi ya yi wannan gargaɗi ne a wani jawabi da aka rabawa manema labarai a Kaduna ta hannun babban sakataren Jama’atu Nasril Islam Dakta Khalil Abubakar Aliyu.

A cewar jawabin Jama’atu ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi ta yi bakin cikin yanda ta ga wasu malamai na kawar da mabiyansu ga abin da a gaskiya kan gubar Korona.

Ya ce a matsayinsu na al’umma dole su kauce wa abin da ƙasar Italy ta yi kar ya faru masana sun ba su shawara kan annobar suka ki.

A jawabin ya ce Sarkin musulmi ya yi kira ga jama’a su yi Azumi a watan nan Sha’aban a roƙi Allah mafita ya kawo ƙarshen annobar.

Ya yi kira ga jami’an lafiya su kula a lokacin da suke kan aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *