Abubuwa 15 da Annabi Muhammad(S.A.W) ya bayyana in aka aikatasu a saurari zuwan Bala’i

Ku Saurari Zuwan Bala’i  ! ! Wata Rana, MANZON ALLAH (S.A.W) YA CE: IDAN AL’UMMATA SU KA AIKATA ABUBUWA GUDA GOMA SHA BIYAR (15), TO A SAURARI ZUWAN BALA’I,

SAI SAHABBAI SU KA CE MENE NE WADAN NAN ABUBUWA YA RASULILLAH?

Sai Manzon Allah (S.A.W) Ya ce:.

1. Idan dukiyar Baitil-Mali ta kasance Ganima ga wasu mutane. A saurari zuwan Bala’i.

2. Idan Amana ta kasance abin cinyewa, wato aka wofintar da ita, ba’a bayar da ita kamar yadda shari’a ta umurta.  A saurari zuwan Bala’i.

3. Idan ma su dukiya su ka dauki Zakka kamar wani Haraji ne aka dora akansu. A saurari zuwan Bala’i.

4. Idan aka wayi gari Mutum ya na girmama abokinsa, ya na wulakanta Mahaifinsa.  A saurari zuwan Bala’i.

5. Idan Mutum ya na girmama Matarsa, yana wulakanta Mahaifiyarsa.  A saurari zuwan Bala’i.

6. Idan aka koma ana koyon Karatun Al – Qurani  ba don Allah ba,  sai don saboda Duniya.  A saurari zuwan Bala’i.

7. Idan ya kasance ana girmama Mutum saboda sharrinsa.  A saurari zuwan Bala’i.

8. Idan ya kasance ana shan Giya iri Daban-Daban.  A saurari zuwan Bala’i.

9. Idan ya kasance ana ado da alhariri bayan Shari’a ta hana. A saurari zuwan Bala’i.

10. Idan ya kasance ana Cudanya tsakanin Maza da Mata ana Rawa. A saurari zuwan Bala’i.

11. Idan ya kasance an bullo da sabbin kayan Kade-Kade da Goge-Goge. A saurari zuwan Bala’i.

12. Idan ka ji ana daga sauti ana hayaniya a Masallatai. A saurari zuwan Bala’i.

13. Idan aka samu Al’ummar karshen zamani suna zagin wadanda suka gabace su. A saurari zuwan Bala’i.

14. Idan Zinace -Zinace su ka yawaita. A saurari zuwan Bala’i.

15. Idan mutane suka halatta cin Riba. A saurari zuwan Bala’i.

An fitar da wannan Hadisin ne a cikin littafin Imamu Tirmizi, daga Ruwayar Sayyidina Aliyu dan Abi Dalib (Radiyallahu anhu).

YA KU YAN UWA MUSULMAI, MENENE DAGA CIKIN WADAN NAN ABABUWAN DA BA YA FARUWA A NAJERIYA?ASHE MUSIBAR DA MUKE CIKI A DUNIYA  MU MUKA JEFA KANMU A CIKI!!.

Allah mun tuba, ka gafarta mana ka kuranye mana musibbun da ke tare da mu.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *