Spread the love

Rahama Abdulmajid sananan marubuciya ce da alƙalaminta ya zagaye ƙasar Hausa wadda wani masani adabi ke yi mata kirari magajiyar Abubakar Imam, ta yi sharhi kan jawaabin shugaba Buhari na basira domin fito da wasu abubuwan da ta fahimta a jawabin da halin da ake ciki a ƙasa.

Wannan shi ne sharhin nata da muka ɗauko a turakarta ta facebook:

Cikin abubuwa 65 da Maigirma kwamandan askarorin Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari ya fada akan mumbarin hudubarsa ta yau, 44 Labarai ne na abinda suka gabata sai Umarni tara masu yiwuwa, sai lallashi guda 3 , sai abubuwa guda uku da ba zasu yiwu ba, sai abubuwa 6 da ko dai ni ban sani ba ko kuma duka yan Najeriya ne basu sani ba.

A gefe daya na ji dadin sanya dokar hana yawo a Biranen da abin ya fi kamari don zai taimaka wajen iya zakulo masu dauke da cutar kafin su ci gaba da yadawa a sauran sassan kasar, duk da an yi matukar latti duk da haka an kara masu awoyi ashirin da takwas Kafin dokar ta fara aiki, kenan zasu iya ketarawa da cutar wani wuri.

Amma inda gizo ke sakar su ne

1 Bincike ya nuna cewa cikin sakamakon da aka samu a kwanaki ukunnnan cutar ta bayyana ne a jikin mutanen da basu je kofa ta kashi ba, kenan tuni har cutar ta zama yar gida wato Local Transmission ya fara aiki, kuma a wannan yanayi hukumar lafiya ta tabbatar da cewa rufe bodoji da hana zirga zirga bai cika cin karfin cutar ba Har ma wani bature likita da sunansa ke wuya ya kira wannan mataki da siyasar da yan siyasa kan yi amfani da ita don nuna wa yan kasa cewa suna aiki tunda dai ba zai sa sisinsu yayi ciwon kai ba. Watakil hakan ta taimaka wa turai fara tunanin kwashe mutanen kasashen waje daga Najeriya kafin yaudarar yan siyasa ta yi ajalinsu musamman a yayinda aka nuna wani mayaudarin gwama a Arewa ya dauki injin ban ruwa a Gona yana ikirarin yiwa jaharsa feshin magani yan jarida na yi masa hoto.

2 Duk da bisa al’ada jawabin shugaba ga yan kasarsa kan kwantar da hankalin talaka, na so a ce zamu ji karin albishir daga Baba Buhari cewa za a bude karin sansanoni gwajin cutar a Arewa duba da an sami karin jihohin Arewa masu dauke da cutar fiye da na Kudu maso kudu wato Benue, kaduna, Bauci. Sai ga shi hukumar na cewa zata kara santa daya ta gwajin a jahar Ebonyi ne ba a Arewa ba wato yankin da ke da masu dauke da cutar kwaya biyar kwatankwacin na Arewa guda 25!

3 Abu na gaba da ke faranta min rai ya kuma razana ni duka a lokaci daya shine yadda masu warkewa daga cutar ke fin masu mutuwa yawa. Lallai cikin mutum 111 da suka kamu a Najeriya 1 tal ne ya mutu zuwa yanzu a cewar hukumomi yayinda mutum 4 suka warke 101 ke zaman mutu kwakwai. Amma ababen damuwar sune

1 Binciken lafiya ya nuna cewa masu warkewa daga cutar kan rayu da marilin huhu da rashin matsarmama wanda watakil ko basu mutu da Coronavirus ba zasu kara jinya ne zuwa gaba mutuwar ta fi sauki ga wasunsu ma.

2 Taruwar da ake a asibitin jinyar cutar ba tare da saurin warkewa ba kan gajiyar da likitoci da injinan yaki da cutar

3 Jan kafar da ake wajen zakulo wadanda suka yi muamala da manyan mutanen da suka kamu da ciwon misali Dan Atiku, Gwamnan Bauci, ABBA kyari, da na baya-bayannan Mal Nasiru Elrufai da Kwamandan Imagireshan Babandede. Wadannan mutane duba da cakuduwarsu da jamaa da kuma saurin yaduwar ita cutar baiyi kama da hankali a ce har yau a cikin mutanen da suka yi muamala da su ba a iya samin mutum 10 da cutar ba.

4 Lallai abin farinciki ne yadda duniya ta dukufa neman rigakafi wa wannan cuta, sai dai wani abu mara dadin ji shine al’adar nan ta dakunan gwajin kimiyya ta cewa basa iya amincewa da magani karbabbe ne sai bayan watan goma sha takwas ake kammala gwada shi, kenan sauran mu wata goma sha biyar kenan idan aka bi ta nasu. Kafin nan ai Coronavirus ta gama da mu tatas! Allah Ya sa ba za abi wannan doka ba tunda lamarin gaugawa ne.

A yanzu dai babu matakin da ya zarce mu Zauna a gida a bar cutar nan a waje ta rasa wanda zata kama! Kuma mu baiwa hukumar lafiya dama ta yi aikinta daidai ruwa daidai kurji.

Managarciya ta kwaso wannan rubutu ne domin ɗimbin hikima da aka zuba a rubutun kuma makarantarmu za su amfana da ilmin marubuciyar da samun ƙaruwa a halin da ake ciki na wannan annobar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *