Spread the love

Har yanzu gwamnatin Sokoto ba ta samar da cibiyar killace masu cutar Korona ba


A binciken da aka gudanar ɗaya daga cikin cibiyoyin da Kwamishinan lafiya Dakta Ali Inname  ya sanar har Gwamnan Sokoto ya ziyarce ta ana kan gininta ne har yau.

Cibiyar da aka samar a asibitin Amanawa a ƙaramar hukumar Dange Shuni a Sokoto 
A ranar Talata data gabata manema labarai sun ziyarci wurin sun samu ma’aikata na kan aikin ka sa riƙa a ƙoƙarin kammla aikin, jami’an lafiyar dake asibitin sun ƙi aminta su yi magana da manema labarai, domin ba su haɗu da shugaban asibitin ba.

Shugaban asibitin koyarwa ta jami’ar Usman Danfodiyo Dakta Anas Sabir ya shaidawa manema labarai ba su da cibiyar killace masu cutar Korona a wirinsu.

Ya ce sai dai gwamnatin jiha ta roƙi buƙatar asibiti ta horas da jami’an lafiya kan harkar Korona.


A asibitin ƙwararru ta jiha Dakta Nuhu Maishanu ya ce  an samar da cibiyar killacewar mai gado 10 a wani gefe cikin adibitin.

Manema labarai sun buƙaci ya nuna masu wurin amma hakan bai samu ba domin ya ce ba a ƙare kammala cibiyar ba, yana sa ran a ƙare sanya kayan amfani a cibiyar da suka samar zuwa Narba(a satin da ya gabata). Har zuwa yau ba a kira manema labarai su shedi samar da cibiyar ba.

Da farko Kwsmishinan lafiya ya ce sun samar da cibiyoyin killacewar guda uku ga wadanda ake zargi da kamuwa ga ciyon Korona.

Ya ce cibiyoyin sun haɗa da asibitin Amanawa, asibitin koyarwa ta Usman Ɗanfodiyo da cibiya ta musamman a asibitin ƙwararru ta jiha.

Wannan jan ƙafar da ake yi bai dace da wannan cutar ba kamata ya yi a ƙara ɗaukar matakin shirin ko ta kwana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *