Ganduje ya hana wata babbar mota da ta kwaso matasa daga Abuja shiga Kano

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kai sumame na ba zata a hanyar Zaria domin ganin yadda aikin rufe hanya da Gwamnatin Jihar Kano ta yi yake tafiya.

Gwamna yayi kaciɓis da wata babbar mota da ta kwaso matasa daga Madalla dake Abuja, nan take Gwamna ya ba da umarnin motar ta koma in da tafito.

Gwamnan ya hana motar shiga garin Kano domin an sanya dokar hana shiga da fita daga Kanon zuwa wasu jihohi a Nijeriya.

Hakan ya nuna duk wani gwamnan da ya sanya dokar kuma bai tafiya cikin sirri don ganin halin da ake ciki a wirin, da wuya shirin ya yi tasiri.

Akwai wani zargi da Managarciya ba ta tabbatar ba yake cewa ko a Sokoto ana samun wannan taka dokar matafiya suna shigowa jihar a ta ɓarayin hanyoyi, in hakan ya tabbata yakamata gwamnati ta dubi lamarin domin ɗaukar matakin da yakamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *