Spread the love

Kasuwar hubbare da ke sokoto kasuwa ce da ta kafu kusan shekaru biyar da suka gabata,kasuwa ce da ake yiwa kirari da kasuwar bi ta tsaye, saboda yawan mutane da ke cin kasuwar kuma  galibi ake gudanar da kasuwanci a tsaye musamman ga masu sayen kaya a kasuwar,ko kuma kasuwar mata Saboda yadda kashi biyu bisa ukku na masu saye da sayarwa a kasuwar mata ne.

Sai dai tun bayan da Hukumar kula da tsara birnin sokoto da ke waye ta bayar da umurnin da katar da kasuwar yau din nan(Alhamis) ta satin nan, domin kasuwar tana ci ne a birnin jihar sokoto duk sati.

Mutane da dama sun yi korafi tare da Allah wadai a kan wannan mataki da suke kallo a matsayin rashin dacewa da aka  yi wa ‘yan kasuwar.

Tun a satin da ya gabata ne kafafen yada labarai na jihar, suka yi ta  sanarwar da katar da kasuwar,abin da ya sanya a safiyar Alhamis ba a yi mamakin ganin jami’an tsaro  da suka yi wa kasuwar kawanya domin hana ‘yan kasuwar yin hada-hadar suka saba.

 ‘Yan kasuwar sun nuna bacin ransu da nuna rashin gamsuwar su ga matakin.

Mai baiwa Gwamnan sokoto shawara a kan tsara birnin sokoto da kewaye Honarabul sidi Abbas, ya bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne domin kaucewa samun matsala duba da yanayin da ake ciki na yaduwar cutar nan da ke kisa ta Korona.

Ya nemi ‘yan kasuwar da su kwantar da hankalinsu wajen bin doka da oda, tare da basu tabbacin cewa idan har al’amurra sun daidaita  kasuwar za ta ci gaba da ci kamar yadda ya kamata. 

Ya kara da cewa ba wannan kasuwar kawai Za’a rufe a fadin jihar ta sokoto ba,a kwai sauran takwarorinta wadan da suka hada da kasuwar marina kasuwar kofar rini da makamantan su.

Daga karshe ya baiwa ‘yan kasuwar hankuri akan yanayin da  dakatarwar zai jefa su. 

 Shugaban kungiyar kasuwar Malam Faruku Mainasara Gidan Haki ya shaidawa wakilin mujallar Managarciya cewa a matsayinsu na ‘yan jiha masu bin doka da oda, ya zama wajibi su bi doka amma kuma rashin adalcin da hukumar ba ta yi musu  shi ne yadda hukumar ta bayar da umurnin dakatar da kasuwar a kurarren lokaci wanda bai fi kwana biyu kasuwar ta fara  ci ba, duba da la’akari da yadda masu cin kasuwar ke fitowa daga wuarare daban-daban daga cikin jihar har ma da makwabtanta wasu ma daga jamhuriyar nijar.

Ya kara da cewar da yawan ‘yan kasuwar sukan bayar da bashi ga kwastomominsu idan sati ya zagayo su biya su sake karbar wani bashi.

Wanda yanzu haka mafi yawan ‘yan kasuwar basu san inda za su hadu da wadanda suke bi bashi ba.

 shugaban ya ce mafiyawan masu cin kasuwar sun dogara ne da kasuwar   shi kansa malamin makaranta ne ta islamiyya, kuma ta hanyar kasuwar ne yake samun abin da ya yi laurorinsa kafin sati ya zagayo.

A saboda haka ya nemi hukumomi da su fito da wani tsari da zai basu damar komawa harkar kasuwancinsu a nan gaba kadan.  Managarciya ta tuntubi wasu da ke sana’a a kasuwar da suka yi jugum bayan dakatar da kasuwar. 

Inna Rabi wata tsohuwa ce da ke sana’ar daddawa (cikin yanayin kuka) ta bayyana cewa, ita ba ta da masaniya da dakatar da kasuwar yanzu tayi hasara,domin ba ta saba cin kowace kasuwa in ba ta hubbare ba. 

shi ma wani matashi dan kasuwa Malam Nasiru Mainasara ya shaidawa wakilin Mujallar managarciya cewa,ba ‘yan kasuwar kawai wannan abin ya shafa ba,harma da su kansu manyan ‘yan kasuwa saboda wadannan; ‘yan kasuwar na hubbare sai sun je babbar kasuwar sokoto, sun sayo kaya wajen su su zo su sayar, saboda haka dakatar da kasuwar su ma ya shafe su.

Ya kara da cewa idan har saboda cutar korona ce ya sanya hukumomi daukar matakin dakatar da kasuwar,  akwai kasuwanni da dama a cikin sokoto wadanda ya kamata a dakatar da su ba wannan kasuwar kawai ba. 

 matashiya Huse dake Sana’ar Jangabu wanda mata ke amfani da shi weajen wankin tukunya, ta bayyana cewa su  an yaudare su da ba’a shaida musu dakatar da kasuwar tun satin da ya gabata ba, domin kuwa duk sati sai sun yi adashe tsakaninsu irin na mata, yanzu haka wannan satin ita ce zata kwashi adashen da suke yi a cikin kasuwar, yanzu ba ta san inda za ta ga takwarorin sana’ar  ta ba, balle ta karbi kudin da ta zuba. 

 Matashi Saminu ya bayyana cewa ba shakka  sun ji dadin tayar da kasuwar duba da irin cunkoson da kasuwar ke haifarwa a duk ranar Alhamis ta mako, abinda ke hana musu gudanar da harkokinsu a unguwar.

Ya kara da cewa ya kamata hukumomi su samarwa ‘yan kasuwar wani waje,domin ko ba komai akan babban titi ne suke wanda ke  zuwa gidan sarkin musulmi,abin da ya kamata a yi tun ba yau ba.   

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *