Spread the love

Tinubu ya nemi Buhari ya dakatar da karɓar haraji don talaka ya samu saukin rayuwa 

Jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya jawo hankalin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sa babban bankin Najeriya, CBN ya buga sabbin kuɗi dan a tseratar da tattalin arzikin Najeriya daga rushewa.


Tinubu yayi wannan magana ne a lokacin bikin tunawa da zagayowar ranar haihuwarshi da ya cika shekaru 68.


Yace ‘yan Najeriya su hada kai da kuma kiyaye abinda zai jawo yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 sosai dan kuwa tsarin kiwon Lafiya na Najeriya ba zai taba iya daukar ace mutane da yawa sun kamu da cutar ba.


Tinubu ya bayar da misalin kasar Amurka  da ke da tsarin lafiya mai ƙarfi amma gashi lamarin yana gagararsu suna shiga cikin matsalar karancin kayan aiki da likitoci.
Ya ce ko wannan ya kamata ya zamarwa Najeriya izina.


Yayi kira ga shugaba Buhari da ya bi sahun kasar Amurka data buga sabbin kudi dan tseratar da tattalin arzikinta daga rushewa, shi ma yasa a buga karin kudin Naira.
Ya kuma yi kira ga Buharin daya dakatar da karbar harajin VAT na dan lokaci ko kuma ya rageshi, ya ce hakan zai taimaka wajan hana tashin farashin kayayyaki dan talaka ya samu sauki kuma za’a samu saukin shigo da kayan masarufi daga kasashen waje.


Tinubu yayi kiran cewa,ita dai cutar nan ba ta bambance addini ko kabila ko kuma  bangaranci dan haka ‘yan Najeriya su hada kai dan yaki da ita.

Masu faɗa a ji a ƙasar nan suna kira ga gwamnati ta bi hanyoyin samun maslaha wanda ake zaton da ta bi ana iya samun sauƙi ga matsalar cutar nan ta Korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *