Spread the love

Shugaban Hukumar Shiga Da Fice Babandede ya Kamu da Cutar Corona Virus.

Kwantrola Janar na hukumar shige da ficen Najeriya, Muhammad Babandede, ya kamu da cutar Coronavirus, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

Kwantrolan wanda ya bayyana hakan ta silar sakon Whatsapp da safen nan ya bayyana cewa tuni ya killace kansa tun lokacin da ya dawo daga kasar Birtaniya ranar 22 ga Maris.

Yace, “A yau, an tabbatar na kamu da cutar COVID-19. Tuni na killace kaina tun lokacin da na dawo daga kasar Birtaniya ranar Lahadi 22 na watan nan ta jirgin British Airways a Legas.

Cutar tana cigaba da yaɗuwa a Nijeriya in da a yanzu manyan mutanen da suka kamu da cutar sun kai biyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *