Spread the love

Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal shugaban majalisar darikar Tijjaniya na jihar Sokoto ya ce Allah ya taimaka maganarsu daya ce a jihar ba wani malamin a cikin wadan da suka halarta a taron masu ruwa da tsaki da gwamnatin jiha ta kira wanda mai alfarma sarkin musulmi ya halarta ya ga dacewar a rufe masallaci da makarantun Islamiyya da ake karanta littafin Allah.

“Rufe masallaci ba daidai ba ne sabon Allah ne, duk aka rufe masallaci Allah ya kori mutane gare shi, duk Allah ya raba mutane in da ake rokonsa ya karba tau azaba zai saukar.” A cewar Farfesa Yagawal.

Ya ci gaba da cewa akwai Malam Dabagin Ardo da ya kawo misallin sallar yaki wadda ke nuna ko a halin tsoro Allah yana son a yi jam’in sallah, dukkan malaman da suka je wurin sun ce abar masallatai bude shi ne daidai da alheri.

Ya ce Ko wace kasa da nata yanayi mu anan Sokoto lamarin bai kaimu can ba, mun ce abar jihar bude jami’an lafiya su tashi tsaye kan lamarin, shi ne aikin da muka yi. “ya rage ga gwamnati ta san dai barin masallaci bude shi ne alheri fiye da rufe shi, rushe masallaci ne rufe shi, don duk abin da ba a rayawa ya rushe, rufe masallatai yafi bala’i fiye da annobar nan ta Korona, in an rufe don kan gwamnati in ta bude kanta.”in Farfesa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *