Fita sallar Jumu’a Shaikh Jingir ya nuna abin da yake fadi har a cikin zuciyarsa ne, Lalon ya gargade shi

Shaikh Sani Yahaya Jingir shugaban majalisar malamai na kungiyar jama’atul Izalatul Bidi’a wa’ikamatus Sunnah mai hidikwata a Jos ya ce shi ba za ki fita sallar jumu’a saboda annobar Korona ba, hakan ko ta faru bayan gwamnatin jihar Filato ta sanya dokar hana yin gangamin mutane da yawansu yafi 50 a dukkan wuraren ibada ko taro a jihar malamin ya jagoranci al’umma suka tafi suka sauke faralin sallar jumu’a.

Jingir ya ce addininsa na musulunci yafi ransa da mahaifansa kuma ya sadaukar da kansa kan addininsa, sallah ita ce kan gaba a addinin musulunci ba zai yi wasa da ita kan annobar Korona.

Wannan abin da Jingir ya yi ya faranta ran musulmai a Nijeriya tare da yin addu’ar Allah ya kare addininsa ga hannun ‘yan bani na’iya, kuma haskensa da bin karantarwa da yake yi a aikace ya karawa mabiyansa kwarin guiwa da tabbacin duk abin da Malam ya fadi har cikinzuciyar shi hakan yake nufi.

Shaikh Jingir wannan abin da ya yi a fahimtarsa hakan yakamata kuma har zuwa lokacin wannan rubutun ba a samu wani da ya warware abin da shaikh ya yi a mahangar shari’a ba.

Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalon ya gargadi malamin kan yunkurin lalata matakan kare mutane da suke dauka a jihar.

Shaikh ya ce sun halarci sallar Jumu’a ne shi da magoya bayansa, saboda gwamnan bai ce kar su je su yi sallah ba.

A jiya Assabar Lalon ya yi bayani wanda sakataren gwamnatin jiha Farfesa Danladi Atu ya sanyawa hannu ya ce gwamnati ba za ta lamunce kin bin umarni da wasu daidaikun jama’a ke yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *