Spread the love

Covid-19 :- Gwamnatin Zamfara Ta Horas da Ma’aikatan Lafiya 100.

Daga Aminu Abdullahi Gusau

A kokarin da take yi na ganin ta dakile bazuwar cutar korona a duk fadin jihar ta, ko da ta shigo cikin jihar.

Gwamnatin jihar Zamfara ta ba da umurnin horas da malaman kiyon lafiya har su 100, kan hanyoyi da dubaru daban daban na yaki da cutar.

Alhaji Nasiru Mu’azu Magarya, shugaban kwamitin wayar da kan jama’a, game da cutar korona a jihar ta zamfara ya bayyana haka yau, a garin Gusau babban birnin jiha.

Shugaban kwamitin ya kara da cewa, za’a dauki likita talatin (30), ya kara da cewa jami’an nas nas guda talatin (30), yanzu haka suna karbar horo na musamman, ta yadda zasu yi mu’ammali da duk abinda ya shafi cutar korona.

Ya kara da cewa ma’aikatan awon jini, guda goma (10) da direbobi goma (10), duk suna nan ana basu horon kamar yadda ya kamata.

Alhaji Nasiru Magarya , wanda har wayau shi ne shugaban majalisar dokokin jihar zamfara, ya kara da cewa, kwamitin su ya zabi Assibitin shan magani ta Damba a cikin karamar hukumar mulkin Gusau, kuma ansa mata sabbin kayan aiki, inda nanne zata zama wajen kebe duk wanda ya kamu da cutar korona.

Haka kuma Assibitin tarayya dake Gusau itama zata zama wajen da za’ayi saurin kai wanda ake tuhuma da wannan cutar, domin tantance shi.

Daga karshe ya ba da tabbacin cewa, kwamitin su zai shiga lungu da sako na wannan jihar, domin su kara fadada aikinsu na fadakar da al’umma, don susan halin da kasa take ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *