Spread the love

Annobar Korona: Zan sake komawa a  yi min gwaji a Legas— Abba Kyari

 
Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa Malam Abba Kyari ya fitar da wani sako daga inda yake a killace, inda ya bayyana cewar zai sake komawa jihar Legas domin sake yi masa gwajin cutar Corona Virus don sanin halin da yak ciki ga cutar.


Malam Abba Kyari ya bayyana cewar yana gudanar da aikinsa ne daga inda yake a kebe tare da taimakawar wasu kwararru da suke taimaka masa gudanar da aikinsa.


“Muna aiki babu dare babu rana, kuma burinmu shi ne samun nasarar wannan gwamnatin ta Shugaba Muhammadu Buhari kuma ba zamu baiwa ‘yan Najeriya da shugaban kasa Muhammadu Buhari kun ya ba”
“Duk da cewar a gwajin da aka yi min na farko sakamako ya nuna ina dauke da wannan cuta da ta addabi duniya, sai dai har yanzu da nake wannan magana ina nan garau, domin ban nuna wani alamun cuta ba a tare da ni.”


“A saboda haka ne, zan sake komawa Legas domin a sake yi min gwajin wannan cuta ta Corona Virus domin sake ganin sakamakon ko ciwon yana nan ko na warke.” A cewar Abba Kyari.


Yanzu dai ‘yan kasa za su sake mayar da hankalinsu ga sauraren sabon sakamakon gwajin da za a yiwa Kyari, domin kamuwarsa na cikin abin da ya kara jefa rudu a Nijeriya da yawan mutane suka tabbatar da ciwon gaskiya ne kuma ya shigo a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *