Kwamitin Fadakarwa domin dakile cutar korona a Zamfara ya fara aiki.

Daga Aminu Abdullahi Gusau

Kwamitin wayar da kai domin kaucewa yaduwar cutar korona a jihar Zamfara ya fara aikinsa kamar yadda ya dace.

Shugaban kwamitin, Honarabul Nasiru Mu’azu Magarya ne ya tabbatar da hakan, alokacin da yake zantawa da ‘Yan jarida game da shirye shiryen kwamitin nasu a gidan sa dake Gusau, babban birnin jihar.

Kamar yanda shugaban kwamitin, wanda kuma har ilayau shi ne shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara yace, wannan kwamiti Gwamnan jiha ne ya Kaddamar da shi

Inda ya kara da cewa, bayan Kaddamar wa, an ba su aiki har kala biyar, sun hada da fadakarwa,ilmantarwa, wayar dakai ta hanyar da za’a dakile bazuwar wannan cutar a fadin jihar, da kuma samar da kebabben wurin da za’a ajiye wanda cutar ta kama.

Alhaji Magarya, ya kara da cewa, domin suga sun dakile bazuwar wannan cutar ta korona, ya zama dole su nemi taimako ga hukumar kiwon lafiya ta Duniya, watau ( WHO ) domin samun dabarun da za’a bi a kaucewa yaduwar cututtuka a wannan jihar.

“Hakama ya zama dole mu nemi taimakon duk masu ruwa da tsaki, kamar sarakuna, uwayen kasa, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu domin kara samun hanyoyin kare kai ga cutar.”inji shi.

Magarya ya kara da cewa kwamitin zaiyi aiki tukuru domin tabbatar da cewa mutanen dake kauyukka an wayar masu da kansu ta yanda zasu kare kansu ga kamuwa da cutar korona.

Shugaban majalisar jihar Zamfara, ya ta’allaka wannan cutar ta( COVID-19 ) a matsayin ibtila’i, mai saurin kisa da ya kewaye Duniya gaba daya.

‘Mu anan jihar, gwamnati ta sayo kayan gwaji, da kuma kayan kariya ga wannan cutar ga mutanen mu, yanzu haka munsa kayan gwaji a duk tashoshin motocin da muke dasu, kuma yau zamuje karamar hukumar mulkin Tsafe domin cigaba da wannan yekuwar. Kuma inajan kunnuwan mutanen mu da suyi amfani da shawar warin da likitoci ke bayar wa, domin kaucewa yaduwar cututtukan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *