Spread the love

Yi wa yara tarbiya ba abin wasa ba ne a tsakanin ma’aurata duk da yanzu lamarin ya dauki sabon salo za ka ga uwaye sun himmatu a yau wajen kai tarbiyar yaransu in da mahaifansu, ma’ana a yau uwaye sun gamsu ‘ya’yansu su zama rikon kakaninsu, kan haka managarciya ta yi hira da wasu uwaye ko sun aminta da wannan yanayi?

Muhammad Sanusi ya ce bangamsu ‘ya’yana su zama rikon kaka ba, mahaifana sun bani kulawa da tarbiya domin na kulla da nawa, ba dalili lokacin da yakamata su huta su ci gajiyar tarbiyar da suka yi min, na mayar da su kasa, don kawai ina son ni in huta na kai ‘yayana wajensu.

Ya ce abin da ba ka sani ba yaran za su sagarce ne domin duk son da ake yi maka nasu zai ninka ne a lokacin da ‘ya’yanka ke gaban mahaifanka, ba su yi masu fada, kuma ba karfin jajircewar da ka samu wajensu, gaskiya zaman yarana wajen mahaifana da raina ba abin da zan gamsu da shi ne ba.

Hajiya Siyama Kabiru mai ‘ya’ya 5 kuma dukansu tana kulawa da su wajenta ta ce, abubuwa ne guda biyu anan rikon kaka da tarbiyar kaka, ina iya kai ‘ya’yana su samu tarbiyar kaka amma ba zan kai su rikon kaka ba, na aminta da tarbiyar da mahaifana suka bani kuma na tabbatar irinta za su baiwa ‘ya’yana, ba wani abin tsoro ga kai diyanka a kula da su wajen mahaifanka don su ne gatanku na farko kafin kowa. Ban gamsu da duk wanda yasan mahhaifansa suna da dabi’a ta son ‘ya’ya ba su yi masu fada ba su son a hantari nasu ya kai diyansa wajensu, rikon kaka ne kawai za su zama.

Najib Salihu shi ma mahaifi ne ya ce bana iya kai yarana wajen mahhaifana domin har yanzu ni ke kulawa da su, to ya kuma zan kai yarana wajensu, ban kuma kai su gidan surukaina domin ba su suka haifamin su ba in har uwayena ba su haifeni ba, uwayen matata ba su haife ta ai ba za mu hadu mu yi aure ba, bana dana sani mu rike diyanmu kamar yadda aka rike mu.

Nana Muhammad mai shekara 34, ta ce ina aminta uwayena su yi wa ‘ya’yana tarbiya tunani ne mai kyau zan yi farinciki diyana suna wajen mahaifana, duba da kyau ka gani tarbiya talalace a wurinmu ba kamar yadda mahaifanmu suka yi mana ba son ‘ya’ya ya hana mu yi masu yanda aka yi mana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *