Spread the love

Na Sadaukar Da Nasararmu Ga  Mutanen Zamfara Matawalle

 Daga Aminu Abdullahi Gusau


Gwamnan Jihar Zamfara  Bello Mohammed (Matawallen Maradun) ya ce ya sadaukar da nasarar da aka samu a kotun koli ga mutanen jihar Zamfara, a jiya(Jumu’a) ne aka yi watsi da karar da APCn Zamfara ta shigar na rokon a sake duba shari’ar da aka yi masu a baya ta gwamnan Zamfara.

 Bello Matawalle ya sadaukar da wannan nasarar ne, a lokacin da yake yi wa zamfarawa jawabi, a gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jihar, jim kadan da samu labarin wannan nasarar da Allah ya ba shi, inda ya ce ya fuskanci kalubale da dama a cikin wata 10, da yayi yana mulki.


Gwamnan ya kara da cewa shi bai taba shakkar komi ba cikin watannin nan da yayi yana mulki, duk da irin kalubalen da yake fuskanta ga ‘yan adawa. Haka ma ya shedawa Zamfara cewa Allah ya ba shi wannan kujera ta gwamna, kuma Shi zai kare mashi ita.


“Kunga a yau din ma anacan ana shari’a, ni kuma inanan gidana kwance ina barci. Sai bayan ankare har an yanke  hukunci sannann aka tayardani daga barci, aka shaidamin cewa an yi watsi da shari’ar domin na tabbatar da cewa Allah ba zai bari a zalunci mutanen zamfara ba.” Matawalle ya ce.


Daga nan sai ya yi alkawarin ba zai ci amana ba, bisa ga nauyin da Allah ya dora masa na shugabantar al’umma.

Ya kara da cewa gwamnati za ta yi  iya kokarinta na ganin ta saukar da nauyin da aka aza  mata  na jagorantar al’ umma .


“Alhamdulillah, tun da yanzu mun kai karshen wannan dambarwar, ina kara kira ga wadanda suka yi fadi tashi wajen warware abin da Allah ya yi, da su zo mu hada hannu domin mu ciyar da jihar mu gaba, ina shaida maku cewa kofa abude take da duk wanda ke son ci gaban Zamfara” ya kammala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *