Kotun ƙoli ta yi watsi da buƙatar APC kan hukuncin Zamfara

Kotun ƙoli ta yi watsi da buƙatar APC kan hukuncin Zamfara


Kotun ƙoli ta Nijeriya ta yi watsi da buƙatar jam’iyar APC a zaɓen gwamnan Zamfara.


A cewar alƙalan kotun ƙolin buƙatar walaƙantar da kotu ne wanda hakan ba za ta saɓu ba.

 Kotu ta tabbatar da hukuncin baya, a kan cewa PDP ce ke da hakkin mallakar jihar Zamfara.


Kuma Gwmana Bello Matawalle Maradun shi ne halastaccen  Gwamnan Jihar Zamfara.


Kotu ta ce masu shigar da ƙara su biya  Milyan biyu-biyu ga waɗan da suke ƙalubalanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *