Spread the love

Kamfanin  BUA ya bayar da tallafin miliyan 300 ga jihohin Sokoto da Edo da Ogun


Kamfanin BUA dake samar da siminti da suga da wasu kayan amfanin yau d kullum a Nijeriya ya ba da tallafin biliyan ɗaya ga bankin ƙasa CBN a yau Jumu’a na shi tallafi domin yaƙar cutar Korona.

Haka kuma Kamfanin mai reshe a jihar Sokoto ya sake ba da wasu miliyan 300 ga jihohi uku, in da jihar Sokoto za ta amfana da miliyan 100, sai Edo ma miliyan 100, Ogun ita ma za ta ɗauki 100 gudunmuwar Kamfanin ga jihohin domin yaƙar cutar dake yawo a duniya COVID-19, a dai ga ba ta yaɗu a jihohin Nijeriya ba. 
Kamfanin ya wallafa sanarwa ne a turakarsa bayan da aka kai tallafin.

Shugaban Kamfanin AbdusSamad Isayaka Rabi’u ne ya jagoranci bayar da tallafin amadadin kamfanin.

Wannan gudunmuwar da attajiran kasar nan ke bayarwa abin a yaba ne don haka zai sa a yaƙi cutar a Nijeriya.

Wasu mutane na ganin irin wannan gudunmuwar ce da gwamnoni ke buƙata a wurin ƙungiyoyi da gwamnatoci da masu arzikin ƙasa da wajenta ne ya sanya gwamnoni ke ɗaukar matakin kariya sosai don dai a tabbatar cutar ba ta shigo cikin al’umma ba, balle har ta zama annoba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *