Spread the love

Hukuncin kotun koli a yau Jumu’a Fargaba ta mamaye magoya bayan APC da PDP a Zamfara

Kotun ƙoli ta sanya yau Jumu’a za ta yanke hukunci kan neman sake duba hukuncin da aka zartar a baya in da jam’iyar APC ɓangaren Abdul’aziz Yari suka sanya a watan mayun shekarar da ta gabata 2019 in da rikicin cikin gida ya haddasa masu rasa kujerunsu.

Kotun ƙoli ta yi hukunci kan APC ba su yi zaɓen fitar da gwani ba kan wannan kotu ta watsar da nasararsu ta baiwa jam’iyar da ta zo na biyu.

Jam’iyar PDP a Zamfara ta amfana da hukuncin in da ta karɓi jagorancin majalisar Zartarwa da ta dokoki a jihar.

Lauyan APC, Robert Clarke (SAN),  ya roki kotu ta sake duba umarnin saboda akwai kurakurrai cikinsa, domin kotun ƙoli kamata ya yi ta umarci APC da hukumar zaɓe su gudanar da zaɓen fitar da gwani, ba wai ta soke nasarar da jan’iyar ta samu ba.

Clarke ya roki kotun ƙoli ta janye hukuncinta don ba PDP ce ta shigar da ƙara ba harkar cikin gida ne aka samu tangarɗa.

Ya faɗa wa kotu, wannan lamari ne kafin zaɓe da aka ɗaukaka ƙara a kutun ƙasa, ba daga Tarabunal ya fito ba, domin a lokacin ba kafa ta ba don ba a yi zaɓe ba, muna ganin hukuncin ba ya da hurumi sai dai a umarci hukumar zaɓe ta gudanar da zaɓen fitar da gwani.

Sashe na 235 a tsarin dokokin ƙasa ya ce kotun Tarabunal ne kaɗai ke da damar yanke hukunci kan matsalar zaɓe, a wannan lamari ba daukaka ƙara aka yi kan matsalar zaɓe ba. Ya wata jam’iya za ta ci gajiyar rikicin cikin gida na APC 

Wannan hukuncin da za a yi ya haifar da fargaba a tsakanin magoya bayan jam’iyyun biyu wanda dai, dole ɗaya ne zai samu nasara ɗayan ya haƙura har zuwa gaba ya nema.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *