Gwamnan jihar Sokoto ya bayyana matsayarsa ta rufe jihar Sokoto daga gobe Jumu’a ba shiga da fice kan iyakokin jihar ta ƙasa da sama har tsawon sati biyu.

Gwamnan Sokoto ya bi sahun takwarorinsa gwamnoni da suka yanke hukuncin rufe jihohinsu, shi ma ya bi sau.

Tambuwal a bayanin da ya yi wa al’ummar Sokoto ya ce kan zaman da aka yi na masu ruwa da tsaki kan haka gwamnati ta yanke hukunci rufe jihar daga gobe Jumu’a zuwa 11 ga watan Afirilu, ƙananan ma’aikata za su yi aiki daga gida.

Tambuwal ya ce a tsawon lokaci ba a yarda zirga-zirga tsakanin wata jiha zuwa Sokoto, masu sana’ar abinci da magunguna kadai aka yarda su shigo jihar daga wata jiha.

sauran bayani zai biyo daga baya……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *