Spread the love

Jam’iyar PDP mai adawa a Nijeriya ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyaya fargabar da ke cikin mutane ya gaggauta yin jawabi kan halin da fadarsa take ciki kan annobar Korona.

Jam’iyar ta nemi a yi hakan ne domin sanin sha’anin lafiya a fadar biyo bayan rahoton da aka samu na shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ya kamu da cutar.

A jawabin da suka fitar a Talata mai magana da yawun jam’iyar Kola Ologbodiyan ya ce jam’iyar ta fahimci a rahoton da aka fitar shugab Buhari ba ya ɗauke da cutar har yanzu akwai bukatar ya yi wa jama’a bayanin halin da ake ciki a fadar.

PDP ta ƙara da cewa Abba Kyari da wasu jami’an gwamnati sun yi tafiya a ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da haɗari a cutar cikin wannan yanayi, haƙƙin shugaba ne ya yi wa ƙasa bayani.

Jam’iyar tana ganin yin jawabin zai janye tuhumar da ake yi wa wasu jami’an kan kiyon lafiyarsu ganin an daina ganinsu a kwanakin nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *