Spread the love

MARTANI ZUWA GA JAM’IYAR PDP AKAN SHIRIN YANKE HUKUNCIN ZABEN JIHAR ZAMFARA

Jam’iyar PDP a mataki na Tarayya Najeriya zuwa mataki na jihar zamfara a halin yanzu duk sun mayar da hankalinsu wajen maganganun hauka, ƙarya da shirme akan shirin yanke hukunci na zaben Jihar Zamfara wanda kotun ƙoli ke shirin gabatarwa kowa ne lokaci.

Saboda haka yana da kyau jam’iyar PDP a kowane mataki dama sauran al’ummar Najeriya su san yanda gaskiyar waɗannan maganganu na ƙarya da PDP suke yaɗawa akan shari’ar zaben Zamfara.

Zaɓen Jihar Zamfara baya da wata alaƙa ta nesa balle ta kusa da jam’iyar PDP, kuma babu inda kotu ko ta ambaci ɓangaren PDP a shari’ar.

Shari’ar ta Zamfara ta ƙunshi wasu ‘ya’yan jam’iyar APC ne waɗanda suke ganin sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyar ta APC bai yi masu daidai ba, don haka suka je kotu neman bahasi.

Waɗanda suka yi wannan ƙara na jam’iyar APC ‘yan ɓangaren Kabiru Marafa, sun nemi gyara ne kawai akan wannan zaɓe na fidda gwani a jam’iyarsu, amma a hukuncin na kotun ƙoli, sai aka ayyana hukunci har wanda ba su nema ba a cikin ƙorafe ƙorafen su na shiga da shari’ar.

Jam’iyar PDP ta samu nasara ne kawai a wannan hukuncin na kotun ƙoli wanda ya shafi jam’iyar APC duk da cewar hukuncin ya zo da ƙalubale wanda ba’a saba gani ba a shari’a, kuma shi ne gyare-gyare wanda Alƙalan Kotun ake sa ran suke nufin gyara akai.

Jam’iyar APC ne ta lashe zaɓe a jihar ta Zamfara a kowane mataki kuma da rinjaye me dinbin yawa, wanda ita kuma jam’iyar ta PDP ta kasa cin ko kashi daya cikin ukku na ƙuri’un da aka zaɓa a zaɓen na zamfara.

Zaɓen Jihar Imo da Bayelsa duk ba su da wata alaƙa da zaɓen Zamfara, domin a zaɓen Imo da Bayelsa sun ƙunshi rikicin jam’iyun adawa biyu ne na APC da PDP, shi kuma rikicin Zamfara ya kunshi jam’iya ɗaya ce ta APC da wasu magoya bayanta.

A zaɓen Jihar Zamfara APC ba ta neman canza dukkan hukuncin kotun ƙoli kamar yanda zaɓen Jihar Imo da Bayelsa suka nema a canza dukkanin hukuncin shari’un nasu biyu baki daya.

Jam’iyar APC a zamfara tana buƙatar ɗan ƙaramin sauyi ne kawai da kuma kwaskwarima ga wasu daga cikin hukunce hukunce na hukuncin shari’ar zamfara (Adjustment of Consequential orders) wanda kotun koli ta ayyana a baya.

Yana da kyau PDP ta san cewar kotun koli ta na da hurumin gyara da kwaskwarima akan hukuncinta na farko idan aka nemi “Review” kuma aka tabbatar da gyaran.

A dalilin haka duk wata farafaganda ko ƙarya ko neman tashin hankali ko barzana wanda jam’iyar PDP take a kan kotun ƙoli da Alƙalan Kotun ƙoli ba zai yi tasiri ba akai kuma Insha Allah za su yi hukunci akan gaskiya.

Ra’ayi: Mutane Masu Kishin Jihar Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *