Spread the love

Majalisar malaman Kano karkashin jagorancin Shaikh Ibrahim Khalel ta fitar da sanarwar ba za ta rufe masallatai ba za a iya cigaba da sallah duba da har yanzu ba wani bayanin samun bullar cutar a jihar Kano.

Shaikh ya ce za a cigaba da gudanar da sallah sai dai masallatanm za su dauki matakan kariya da jami’an lafiya suka bayar kamar zuba man wanki hannu ga masallata waton Sanitaza da kyallen rufe baki da hanci.

Shugaban ya ce bai kamata a rufe masallatai ba hasalima ya yi kira ga mutane su dukufa ga yin addu’ar samun saukin wannan annobar.

Gwamnatin jihar Kano ta rufe iyakokinta na kasa abin da ke nuna motoci dake wajen jihar ba za su shigo cikin jihar ba, akwai yiwuwar lamarin jihar zai tsaya cik saboda daukar matakin kariya daga annobar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *