Covid-19: Gwamnatin Zamfara Zata Rufe Iyakar ta Da Sauran Jihohi Makwabta.

Daga Aminu Abdullahi Gusau

A kokarin sa na kare jama’arsa ga kamuwa da cutar nan ta korona, Gwamnan Zamfara Bello Muhammed Matawalle, ya ba da dokar rufe duk iyakokin jiharsa.

Gwamna Matawalle ya bada umurnin ne yau(Alhamis) a lokacin da yake jawabi ga yan jaridu dangane da karin matakan da gwamnatinsa ta dauka domin dakile bazuwar wannan cutar.

Ita dai jihar ta Zamfara tayi iyaka da Jihohin Sakkwato, Kabi, Katsina, da kuma jamhuriyar Nijar.

Ya kara da cewa wannan dokar zata fara aiki ranar Assabar, inda yace rufe iyakar na sati biyu ne kawai kafin aga abinda Allah zai yi, haka zalika ya tunatar da jama’a cewa duk wanda yake son fita ko shiga a Zamfara to gobe ne kawai ya rage masa.

Bello Matawalle ya sanarda da cewa wannan dokar bata shafi masuyin jirga jirga na cikin jiha ba, kuma ya lurar da jama’a cewa, wannan dokar anyi tane domin kariya ga mutane, badon a kuntata masu ba

“Duk gwamnatin da tasan abinda takeyi, to ya kamata tasa tsaron lafiya da kare rayuwa da dukiyoyin jama’arta, bisa ga wannan ne mukaga ya dace mu kara daukan matakai bayan wayan da muka dauka a baya.”

A don haka mun tanadi magani mai yawa, da kuma kayan gwajin wannan cutar, haka zalika munyi kwamiti har guda biyu wayanda muka azawa nauyin fadakar da mutane da kuma bada shawara ga gwamnati, domin bada tallafin gaggawa in bukatar hakan ta faru.”.Inji Gwamna.

Saboda haka Gwamna Matawalle yaja kunnen mutane da suba wannan dokar goyon baya, domin za’asa jami’an tsaro ko wane lungu da sako domin su tabbatar babu motar data shigo ko ta fita wajen wannan jiha.

Wannan taron na manema labarai an yishi ne a gaban shuga bannin tsaro dake wannan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *