Spread the love

Kwamitin Malamai  da gwamnatin  Sokoto ta kafa sun cimma matsaya  kan annobar Korona baros

Daga Muhammad Muhammad

Kwamitin malalamai da gwamnatin jihar Sokoto ta kafa bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a fadar gwamnatin jiha wanda Gwmna da mataimakinsa da Sarkin musulmi suka halarta ya cimma matsaya kan cutar Korona baros a matakin da gwamnati za ta ɗauka.

Malaman da suke cikin kwamitin dukansu sun aminta da matsayar gwamnatin sokoto kar ta rufe masallatan Jumu’a da na yin salloli biyar da makarantun islamiya da kasuwa.

Haryanzu bayan kammala aikin kwamiti gwamnati ba ta fitar da matsayarta kan goyon bayan matsayar malamai ko akasin haka.

Ba daidai ba ne a rufe masallaci kai  saɓon Allah ne ma, in aka kori mutane gaban Allah azaba na iya saukar.  A cewar Farfesa Abubakar  Yagawal ɗaya daga cikin malaman da ke cikin kwamitin da gwamnati ta kafa.

Ya ce  kowa nada nasa  yanayi su anan Sokoto lamarin bai kai can ba, sun ce abar Sokoto buɗe jami’an lafiya su tashi tsaye kan lamarin.

Ya ce barin masallaci buɗe shi ne alheri fiye da rufe shi, rushe masallaci ne in an rufe shi,  duk abin da ba a rayawa ya rushe. Rufe masallatai yafi bala’i fiye da annobar nan ta Korona.

Shaikh Abubakar Usman Mabera shugaban majalisar malamai na Izalatul bidi’a Wa’iƙamatus Sunnah mai hidikwata a Jos ya ce annobar dai bisa ga abin da ake da masaniya kan shi babu ta a Sokoto.

Yace ‘kan haka muka ce anan Sakkwato ba damar hana sallar Jumu’a, dama ce ma ta rokon Allah don sabon Allah ne ya haifar da ita, mu zo masallaci don hanya ce ta kusantar Allah. Mun yi ittifaki masallatanmu na jumu’a za a ci gaba da sallah da sauran salloli, makarantunmu kuma za mu ci gaba da karatu da rokon Allah ya yaye wannan musibar.” a cewarsa.

Mabera yana cikin ‘yan kawamiti ya ce za su ci gaba da bin shawarar malaman lafiya a wajen inganta tsaftarsu musamman ta wanke hnnu duk da su musulmai ne suna alwala.

Kwamitin na kusan malamai 10 da sakataren gwamnati da kwamishinan lafiya suna cikin ‘yan kwamitin kuma sun halarta a zaman.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *